‘Ko Buhari Ba Zai Fara Tunanin Ba Ni Shugaban Fadarsa Ba’

0
432
Marigayi Abba Kyari,. Ko wane ne zai kwafe ggurbinsa?

Rahoton Z A Sada

DAYA daga cikin mutanen da ake rade-radin cewa suna cikin makusantan shugaban Najeriya da za su iya maye gurbin Malam Abba Kyari, ya ce lokaci ya wuce ga mutum irinsa ya karbi wani aikin gwamnati.

Alhaji Ismaila Isah Funtua ya ce: “Abin da na ji a raina…Na dauki wannan jita-jita (a matsayin) wulakanci. An wulakanta ni”.

Ya ce lokacin da aka kori gwamnatin farar hula a 1983 (Jamhuriya ta biyu) yana minista. “Har wani yau ya yi tunanin a kawo sunana cikin (wadanda za a iya nadawa) shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa?”

Tun bayan rasuwar Malam Abba Kyari ranar Juma’a ne, wasu mutane suka fara zayyana sunayen wasu makusantan Shugaba Buhari, suna cewa a cikinsu ne za a nada magajin Abba Kyari.

Shi dai Isma’ila Isah Funtua na cikin manyan mutane guda uku da ake ganin na-hannun dama ne ga shugaban Najeriya, hasali ma su ne wasu ke wa lakabi da ‘cabal’ wato su ne ke kulla komai na gwamnati mai ci. Kodayake, tsohon ministan ya sha musanta wannan ikirari.

Isma’ila Funtua ya ce: “Na yi aikin En’E, na yi aikin gwamnati, na siyasa har na tashi na kai matsayin minista a kasar nan”. Mutumin da ya yi minista 1983 zuwa yau kusan shekara nawa ke nan? An tasam ma shekara 40. Kuma sai a ce wai ka je a nada ka mukami. Wanne aiki za a ba ni, ni yanzu?” In ji shi.

Ya ce ai ya fi karfi a ba shi wani aiki. “Ni mai daukar mutane aiki ne, tun da na kafa wuraren da jama’a za su samu abinci da iyalansu”.

A cewarsa shedanci ne ya sa wasu kawai suke kama sunan wani jigo su ce a ba shi aiki don kuwa ba sa la’akari da abubuwan da ya yi a baya, da kuma ko zai iya aikin, ko ma ya fi karfin da ake ambata.

“Irin abin nan ne da ake cewa mutum ya wuce lokacin da za a ba shi aiki. Aiki yanzu ai sai ‘ya’yanmu ko kannenmu,” in ji Alhaji Isma’ila Funtua.

Ya bukaci ‘yan Najeriya masu irin wannan tunani su rika mutunta kawunansu da kasarsu.

A cewarsa idan mutum irinsa kullum zai makale a gwamnati sai ta ba shi aiki, to me suke so ‘ya’yansu da kannensu su yi.

An tambaye shi, to idan Shugaba Buhari ya bukaci ya karbi mukamin don ya taimaka wa gwamnatinsa. Sai ya ce shi ma ba zai fara ba, “don ya san ba zan karba ba”.

Isma’ila Funtua ya ce Najeriya ba ta yi lalacewar haka ba, a cewarsa masu rade-radin suna mayar da sha’anin mulkin kasa kamar wasa.

“Idan ka duba ma sunayen da suke rubatawa. Haba jama’a!”

Ya ce idan yau kana da aikin kwamiti, ka duba mutum irina da wadansu “daidai da ni da wadanda suka fi ni, ka ce don Allah ku duba abu kaza ku ba ni shawara. Sai a yi, a ba ka shawara.”

“Amma dai ba dai mu yi aiki a ce a ba mu albashi ba,” in ji Isma’ila Funtua.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here