Dan Gwagwarmaya I . G Wala Ya Samu Afuwar Shugaban Kasa

0
242

Daga Usman Nasidi.

DAN gwagwarmaya, Ibrahim Garba Wala, wanda aka fi sani da ‘IG Wala’ ya shaki iskar ‘yanci bayan an kulle shi a kurkuku na tsawon shekara biyu.

Wata kotun Najeriya ce ta tura IG Wala gidan yari bayan samunsa da laifin gaza gabatar da hujja a kan zargin wani jami’in gwamnati da cin hanci.

An saki IG Wala ne bayan afuwar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi wa fursunoni 2,600 a fadin Najeriya.

Jastis Yusuf Halilu na babbar kotun tarayya da ke Abuja ne ya yankewa IG Wala hukunci ranar 15 ga watan Afrilu na shekarar 2019.

Kotun ta yanke wa IG Wala hukunci ne bayan shugaban hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON), Abdullahi Mukhtar, ya shigar da kararsa a kan yi ma sa kazafin cin hanci.

A cikin takardar kara da Mukhtar ya shigar a gaban kotu, ya yi zargin cewa IG Wala ya yi amfani da dandalin sada zumunta (facebook) wajen bata ma sa suna da zubar ma sa da mutunci da na hukumar NAHCOM.

A ranar 17 ga watan Satumba na shekarar 2017 ne IG Wala ya wallafa a shafinsa na ‘facebook’ cewa Mukhtar ya samu biliyan N3 ta haramtacciyar hanya daga kudin maniyyata aikin Hajji.

Dan gwagwarmayar ya fada tsaka mai wuya ne bayan ya gaza gabatar da wata hujja da za ta nuna gaskiyar zargin da ya ke yi wa Mukhtar.

A cikin watan Maris na shekarar 2020, kotu ta rage tsawon wa’adin zaman gidan yarin da IG Wala zai yi daga shekara bakwai zuwa shekara biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here