Jihohin Kudu Maso Yamma Za Su Kaddamar Da Dokar Bai Daya

0
332
Mustapha Imrana Abdullahi
JIHOHIN yankin Kudu maso Yammacin tarayyar Nijeriya na shirin kaddamar da dokar bai daya a kan yin amfani da Takunkumi ga kowa da ya samu kansa a jihohin yankin.
Kamar yadda Gwamnaonin suka sanar cewa a halin yanzu suna nan a kan kokarinsu na samar da miliyoyin Takunkumin rufe baki da hanci ankokarinsu na yaki da cutar Covid – 19.
Kamar yadda Gwamnan Legas Babajide sanwo Olu ya shaida wa manema labarai cewa tuni su sun yi nisa wajen kokarin samar da Takunkuman ta hanyar yin amfani da Telolin cikin gida da suke dinka miliyoyin wadannan Takunkumai da za a yi amfani da su cikin satin nan.
“Za mu mayar da lamarin yin amfani da Takunkumi ya zama dole ga dukkan jama’ar yankin, kamar yadda kuke gani a halin yanzu dukkanmu tun daga kaina har ya zuwa dukkan wanda ke tare da ni muna amfani da Takunkumin da aka samar ne a cikin gida da Telolinmu sula Dinka, kuma muna ci gaba da samar da miliyoyin Takunkumai domin rabawa jama’a su yi amfani da shi don haka kada jama’a su damu kansu wajen sayen Takunkumin rufe baki da hanci a kokarin yaki da cutar Covid – 19 da ake kira Korona bairos.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here