Korona Bairos Na Kara Yaduwa A Makkah Da Madina

0
600

Rahoton Z A Sada

MA’AIKATAR lafiya a Saudiyya ta ce mutum 1,147 sun kamu da cutar korona a rana daya, inda yanzu adadin yawan wadanda suka kamu da cutar ya kai 11,631 a kasar.

Kamfanin dillacin labaran SPA ya ce an samu karuwar cutar a ‘yan kwanakin da suka gabata sakamakon karuwar gwaji da ake yi, kamar yadda kakakin ma’aikatar lafiya na kasar ya bayyana a wani taron manema labarai.

Kawo yanzu mutum 109 aka tabbatar da cutar korona ta kashe a Saudiyya. Mutum 1,640 suka warke zuwa yanzu.

A Makkah cutar ta fi yaduwa inda mutum 305 suka kamu, sai Madinah inda 299 suka kamu sai kuma 171 a Jeddah, 148 a Riyadh.

Ministan lafiya na Saudiyya Dokta Tawfiq Al-Rabiah ya yi gargadin cewa yawan masu cutar za su kai sama da 200,000 cikin makwanni.

Tuni hukumomin Saudiyya suka hana shiga Makkah da Madina, da ma Riyadh babban birnin kasar, a kokarin da hukumomin kasar ke yi na hana yaduwar Covid-19.

Ana fargaba kan yiyuwar gudanar da aikin hajji a bana, yayin da cutar korona ke ci gaba da yaduwa.

Kwanaki suka rage al’ummar Musulmi su fara Azumin Ramadan, a cikin wannan yanayi da aka killace kusan al’ummar duniya saboda annobar cutar korona inda sama da mutum miliyan biyu suka kamu da cutar a duniya.

Kuma Saudiyya ta kara daukar matakai kamar haka:

  • Babu jam’in sallar asham kamar yadda aka saba, ma’aikatan masallacin harami ne kawai za su yi Sallah.
  • An rake yawan raka’o’in Sallar asham zuwa 10, kuma za a takaita addu’a (Kunut) kafin sallame wutiri.
  • An soke shan ruwa a Masallatan harami na Makkah da Madina.
  • An dakatar da umrah lokacin azumi
  • Za a sauke Al Qur’ani kamar yadda aka saba amma a Sallolin Asham da Tuhajjud

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here