Kwamanda Bakori Zai Bunkasa Ayyukan Kungiyar Banga Ta VGN-‘Yan Kugiya.

0
564
Jabiru A Hassan, Daga Kano.

Navy Captain A. B. Bakori, Babban Kwamanda VGN Na Kasa.

AN bayyana cewa  sabon babban  kwamandan kungiyar banga ta Vigilante group of Nigeria(VGN), Navy Capt. A. B. Umar Bakori mai ritaya zai kara bunkasa aiyukan kungiyar tareda bullo da Karin hanyoyi na kyautata  tabbatar da tsaro a fadin kasa baki daya.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin wasu yayan kungiyar a karshen wani aikin tsaro da suka yi a Kano, inda suka nunar da cewa kafin sabon babban kwamanda Bakori ya kama aiki an sha gwagwarmayar rikice-rikicen cikin gida a kungiyar ta VGN, wanda kuma hakan ya dabaibaye ci gaban harkokin kungiyar tareda kawo rabuwar kawuna tsakanin mabobin ta.
Malam Haruna Liman, kwamandan kungiyar na yankin Kunnawa-Dungurawa dake yankin karamar hukumar Dawakin Tofa, ya shaidawa wakilin mu cewa yanzu kungiyar VGN ta zamo a dunkule, kuma kowa ya hakikance cewa sabon kwamanda Bakori zai kara samar da masalaha tsakanin yayan kungiyar da sauran jagororin ta a duk inda  suka domin tafiya bai daya.
Sannan yayi fatan cewa dukkanin yayan kungiyar ta VGN zasu baiwa babban kwamanda A. B. Umar Bakori goyon baya da hadin kai ta yadda kwalliya zata ci gaba da biyan kudin sabulu, haka kuma yayi addu’a ga marigayi tsohon kwamanda Dokta Ali Sakkwato tareda fatan Allah ya gafarta masa ya kuma sadashi da rahama bisa aikin alheri da ya yiwa al’uma.
Wakilin mu ya gudanar da wani jin ra’ayin al’uma inda ya ruwaito cewa ko shakka babu, sabon babban kwamanda kungiyar ta VGN Navy Captain A. B. Umar Bakori zai kara inganta wannan kungiya tareda dora ta kan sahihiyar hanyar taimakawa jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a tsare dukiyoyin al’umar Nijeriya, tareda fatan cewa gwamnatin tarayya da na jihohi da su taimakawa wannan kungiya muhimmiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here