Mai Tsaron Lafiyar Shugaba Buhari Ya Rasu

0
319

Rahoton Z A Sada

MUN sami labarin cewa, daya daga cikin masu tsaron lafiyar Shugaba Buhari na Najeriya ya rasu

Mai taimaka wa shugaba Buhari kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ne ya sanar da hakan a Twitter ranar Talata.

Bashir Ahmad ya ce Lawal Mato ya rasu ne sakamakon ciwon suga da ya shafe shekara uku yana fama da ita.

Sanarwar ta ce ya rasu ne ranar Talata. Mato ya dade yana aiki da Shugaba Buhari tun kafin ya zama shugaban Najeriya a shekarar 2015, kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.

Wata ‘yar uwar mamacin da ta nemi a sakaya sunanta ta ce mana ya rasu ne a Kano bayan ya dan yi fama da rashin lafiyarsa ta ciwon suga a wani asibiti da ke birnin.

Dan ainihin garin Maigatari na jihar Jigawa, kuma a can aka yi jana’izarsa da yammacin Talata.

Ya mutu ya bar mata daya da yara bakwai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here