Sabbin Mutane 117 Sun Kamu Da Coronavirus A Legas, Abuja Da Kano

0
416

Daga Usman Nasidi

CIBIYAR takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane 117 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Talata, 19 ga Afrilu, 2020.

Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra’ayinta na Tuwita inda tace: “An samu karin mutane dari da sha bakwai (17) sun kamu da #COVID19″

Mutane biyar da aka ruwaito sun kamu a Legas, an mayar da su jihar Ogun. Saboda haka yanzu Legas mutane 430 take dashi, Ogun kuma 20.

Kawo karfe 11:25 na daren 21 ga Afrilu, mutane 782 suka kamu da cutar COVID-19 a Najeriya.

An sallami: 197
Mutuwa : 25

Jahohin da aka samu karin mutane dari da sha bakwai din sun hada da:

Mutane 59 a Jihar Legas
Mutane 29 a Babban Birnin Tarayya
Mutane 14 a Jinahr Kano
Mutane 6 a Jihar Borno
Mutane 4 a Jihar Katsina
Mutane 3 a Jijar Ogun
Mutum 1 a Jijar Ribas
Mutum 1 a Jihar Bauchi

Ga jerin sunayen duka jihohi da adadin yawan mutanen da suke dauke da Cutar Koran a Kasar Najeriya.

Lagos-430
FCT-118
Kano-73
Osun-20
Ogun-20
Oyo-16
Katsina-16
Edo-15
Kwara-9
Kaduna-9
Akwa Ibom-9
Borno-9
Bauchi-8
Gombe-5
Delta-4
Ekiti-4
Ondo-3
Rivers-3
Jigawa-2
Enugu-2
Niger-2
Abia-2
Benue-1
Anambra-1
Sokoto-1

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here