Shugaba Buhari Zai Yi Jawabi Mai Zafi A Mako Mai Zuwa – Shugaban NCDC

0
252

Daga Usman Nasidi.

DARAKTA janar din hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa, Dakta Chikwe Ihekweazu ya sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu zai bayyana wasu tsauraran hukunci a kan yakar annobar Coronavirus a mako mai zuwa.

Ya ce: “A ranar Laraba mai zuwa ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi wayar tarhon hada ja da gwamnoni kuma zai sanar da wasu tsauraran matakan a kan tattalin arziki.”

Shugaban NCDC din ya sanar da hakan ne a yayin da ya kai ziyarar ban girma ga Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari a gidan gwamnatin jihar da ke Katsina.

Ya yi jawabi ne a yayin da gwamnan ya bukaci kafa wurin gwajin cutar a Katsina don gaggauta samun sakamakon wadanda ake zargin suna dauke da cutar a jihar.

Masari ya ce ana tafiyar sa’o’i 12 daga jihar kafin a samu wurin gwajin kwayar cutar a Abuja.

Ya ce: “Samar da dakin gwajin cutar a jihar zai taimaka wajen rage tsawon lokacin samun sakamako da kuma wahalar da muke sha a yayin kaiwa.

“Samfurin jini idan an diba a Katsina suna daukar a kalla sa’o’i 24 kafin su isa Abuja a samu gwada su.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here