‘Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji 4 A Karamar Hukumar Zurmi Da Ke Zamfara

0
619

Daga Usman Nasidi

WASU wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe sojoji hudu a karon da suka yi a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Wata majiya wacce ta san yadda lamarin ya faru ta sanar sa cewa sojojin na kai kayayyakin abinci ne ga abokan aikinsu da ke cikin daji.

An gano cewa ‘yan bindiga sun biyo sojojin ne a cikin daji wanda yake kusa da kauyukan Garin-Kada da Birane da ke karamar hukumar Zurmi ta jihar.

Ya ce, “Sun yi amfani da rashin kyan hanyar da ke cikin dajin inda suka labe har zuwa isowar dakarun. Babu jimawa kuwa suka bude wa ababen hawarsu wuta.

“Bayan budewa dakarun wuta, sun kashe hudu daga ciki a nan take. Amma kuma, sojojin sun halaka ‘yan bindigar masu tarin yawa tare da kwace makamansu.

“Kwamandan rundunar Operation Hadarin Daji , Birgediya Janar Aminu Bande ya kai ziyara wurin da lamari ya faru.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here