Kamfanin KEDCO Zai Ci Gaba Da Samar Da Ingantacciyar Wutar Lantarki A Jihohin Kano Da Jigawa Da Katsina.

0
667
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
KAMFANIN Samar da wutar lantarki watau KEDCO, yayi alwashin ci gaba da bada ingantacciyar wutar lantarki a jihohin Kano da Jigawa da kuma  Katsina musamman a wannan lokaci da make ciki na zama a gida don rigakafin annobar Covid-19 wadda ake fama da ita a fadin duniya.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Larabar nan 22-4-2020, wadda kuma babban jami’in sadarwa da Hulda da jama’a na kamfanin  Malam Ibrahim Sani Shawai ya sanya wa hannu, kamfanin na KEDCO ya bayyana cewa ana kara daukar kyawawan matakai da kuma hanyoyi na inganta bada wutar mai inganci tare da sharewa abokan hulda hawaye dangane da abubuwan da suka shafi kamfanin domin bunkasa zamantakewa a yankunan karkara da birane.
Haka kuma kamfanin ya sanar da cewa kasancewa yanzu ana zaune a gudaje bisa umarnin gwamnati kan cutar Corona Virus, an fitar da wasu hanyoyi  mafi sauki domin samar da wani dandali na saduwa tsakanin kamfanin na KEDCO da abokan huldarsa a tsari iron na fasahar sadarwa wadda yanzu itace a sahun gaba wajen gudanar da mu’amulla cikin sauki da gamsarwa.
 Sanarwar ta bayyana hanyoyin da kamfanin ya fito dasu domin ci gaba da saduwa da abokan huldarsa wadanda suka hada da:www.kedco.ng/payment, da www.powershop.ng da www.arewaelectricity.com ko kuma a ziyarci shafin Dada zumunta a kedco@tweeter da kuma kedco plc in Facebook ko kuma kai tsaye  zuwa customercare@kedco.ng domin bayyana was kamfanin abubuwan da ake da bukata.
Haka kuma sanarwar tace kamfanin yana kira ga al’umomin jihohin Kano da Jigawa da Katsina da su ci gaba da ba da rahoton duk wata matsala da suke ganin ta faru kan layukan su na wutar lantarki ta yadda za a gaggauta gyara su da kuma kyautata yanayin su domin ba da wutar mai inganci kamar yadda abin yake cikin manufofin kamfanin na KEDCO.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here