
Isah Ahmed Daga Jos
KARAMAR Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, ta tallafa wa mutum 170, maza da mata da injinan markade da kekunan dinki da injinan ban ruwa, domin su sami sana’ar da zasu dogara, da kansu. Karamar hukumar ta raba wadannan wadannan kayayyakin ne, a Sakatariyar karamar hukumar da ke garin Saminaka, a ranar talatar nan.
Da yake jawabi a lokacin da yake mikawa wadannan mutane kayayyakin, shugaban karamar hukumar Alhaji Abubakar Buba, ya bayyana cewa ganin irin matsanancin halin da jama’a suke ciki ne, ya sanya suka dauki wannan mataki na tallafa masu. Domin su riqa samun abin da zasu riqe kan su, da iyalansu.
Ya ce mutum 170 ne suka amfana da wannan shiri, kuma karamar hukumar ta kashe kudi sama da naira miliyan uku, wajen sayen wadannan kayayyaki.
Ya yi kira ga wadanda suka sami wadannan kayayyaki, suyi amfani da su kamar yadda ya kamata, kada su je su sayar. Domin an ba su wadannan kayayyaki ne, domin su je su yi amfani da su, wajen samun abin da za su rike kansu da iyalansu.
Ya yi kira ga al’ummar karamar hukuma su rika bin shawarwarin da jami’an kiwon lafiya suke bayarwa, kan kare yaduwar annobar cutar korona da ake fama da ita, a halin yanzu. Kuma duk inda suka ga alamun wannan cuta a karamar hukumar, su sanar da hukuma domin a dauki matakin gaggawa.