Korona Bairos: Gwamnan Kaduna Nasir Elrufa’i Ya Warke

0
415

Rahotn Z A Sada

GWAMNAN jihar Kaduna, Malam Nasiru Elrufa’i ya ce ya warke daga cutar korona bayan shafe kusan wata ɗaya yana killace.

Malam Nasir Elrufa’i ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce “Ina farin cikin sanar da ku a yau cewa bayan kusan makonni hudu ina karbar magani, yanzu na warke daga cutar bayan gwaje-gwaje guda biyu da aka gudanar sun nuna ba na ɗauke da cutar.

Gwamna El-Rufai ya sanar da cewa ya kamu da cutar korona ne ranar 28 ga watan Maris.

Shi ne mutum na farko da cutar ta kama a jiharsa ta Kaduna, yayin da yanzu mutum 9 hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta ce sun kamu da cutar a Kaduna.

Mataimakiyar gwamnan jihar, Dr Hadiza Balarabe ce ta ci gaba da tafiyar da harakokin gwamnatin Kaduna.

Bayan sanar da labarin warkewarsa, gwamnan ya godewa mataimakiyarsa Dr Hadiza Balarabe kan jajircewarta wajen tafiyar da harakokin gwamnati a lokuttan da yake jinyar cutar korona.

Shafin Twitter na gwamnatin Kaduna ya wallafa cewa bayan sallamar gwamna Elrufa’i, nan take ne kuma ja jagoranci tattaunawa da kwamitin da ke yaƙi da cutar korona a jihar, kafin kuma ya shiga taron kungiyar gwamnoni ta intanet.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here