A’isha Buhari Ta Jinjina Wa Matan Tsoffin Shugabannin Kasa A Kan Gudunmawa

0
292

Daga Usman Nasidi.

A RANAR Alhamis uwargidan shugaban kasa, A’isha Buhari ta wallafa sakon godiya da fatan alheri a shafukanta na sada zumuntar zamani.

Aisha Buhari ta mika godiyarta ga matan tsoffin shugabannin kasa da irin tallafin da suka ba da don yakar annobar Covid-19 a kasar nan.

Ta mika godiyarta ga matan tsoffin shugabannin kasa da suka hada da Patience Jonathan da ta bada cibiyar killacewa, magunguna da kuma kayan kariya ga ma’aikatan lafiya.

Ta kara da cewa za a yi amfani da kayayyakin yadda ya dace kuma za a raba su zuwa inda ya dace.

“Ina son mika godiyata ga wa danda suka amsa kiranmu don taimakawa wajen yaki da cutar Covid-19.

“Ina godiya ga ‘yan Najeriya ballantana matan tsoffin shugabannin kasa a kan sakonnin alherin da kuma gudumawa da suka bada.

“Ina godiya ga Dame Patience Jonathan da ta bada otal dinta wanda yake kotu a kan a yi cibiyar killacewa da shi na wucin-gadi.

“Duk kayayyakin da aka bada da suka hada da gadajen asibiti, zannuwan gado, kayayyakin kariya da kuma magunguna, za a raba su da gaggawa,” ta ce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here