Ko Makiyina Ba Na Masa Fatar Samun Cutar Covid-19 – El-Rufa’i

0
408

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

A RANAR Laraba ne Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa’i ya ce ya warke daga muguwar cutar coronavirus bayan gwaji har kashi biyu sun nuna babu cutar a tare da shi.

El-Rufa’i a matsayin wanda ya yi nasarar samun lafiya, ya kwatanta cutar da babban kalubale ga jama’a.

Ya ce ba zai yi wa babban makiyinsa fatan samun cutar ba, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

A jawabin kai tsaye da gwamnan ya yi ga jama’ar jihar, ya ce, “Ina matukar farin cikin sanar da ku cewa yau Laraba ta tabbata bana dauke da cutar coronavirus bayan gwaji na biyu da aka yi min.”

Ta tabbata gwamnan na dauke da cutar ne a ranar 28 ga watan Maris bayan gwajin da aka yi masa ya nuna hakan.
Ya killace kansa karkashin kulawar masana kiwon lafiya inda yake karbar magunguna.

El-Rufa’i ya ce masana kiwon lafiya a karkashin ma’aikatar lafiya ta jihar da asibitin koyarwa na Barau Dikko ne da ke Kaduna suke kula da shi.

A kalamansa: “Ina mika godiya ga Ubangiji tare da godiya ga sakonnin nuna kulawarku, addu’o’i da kuma goyon bayanku bayan na tabbata dauke da cutar.

“Ba firgici kadai iyalaina suka shiga ba, sun fuskanci barazanar kamuwa da cutar. Dukkan iyalaina sun goyi bayana kamar yadda suka saba.

“Abokaina da ‘yan uwa da ke dukkan sassa na duniyar nan sun turomin da sakon fatan alheri da addu’o’in samun sauki.

“Ina mika godiyata ga zakakuran ma’aikatan lafiya da kuma hukumar asibitin koyarwa na Barau Dikko, wadanda suka kula da ni ta hanyar jajircewarsu da iyawar aikinsu.”

Ya kara da cewa, “Abun farin ciki ne ganin kokarin kwamitin yaki da cutar ta jihar Kaduna wanda ya samu shugabancin Dakta Hadiza Balarabe, ma’aikatar lafiya da sauran masu ruwa da tsaki ta yadda suka jajirce.

“Ina jinjina ga mataimakiyata ta yadda take jagoranci duk da bana nan. A wannan lokacin, manyan jami’ai sun nuna kokarinsu da kwarewarsu a shugabanci.”

Gwamnan ya kara da cewa, akwai bukatar sauya wasu daga cikin dokokin killace kai a jihar. Daga yanzu dole ne kowa ya dinga amfani da takunkumin fuska a yayin fita daga gida ko zuwa wurin aiki.

Ya kara da cewa, gwamnati za ta samar da takunkumin fuska ga talakawa da kuma masu bukata a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here