Ma’aikatan Asibiti 40 Suka Kamu Da Cutar Korona A Najeriya

0
207

Daga Usman Nasidi.

MINISTAN kiwon lafiyan Najeriya, Osagie Ehanire,ya bayyana cewa Ma’aikatan asibiti 40 suka kamu da cutar coronavirus a yayin ceto rayukan mutane.

Osagie Ehanire, ya bayyana hakan ne yayin hirar kwamitin kar-ta-kwanan fadar shugaban kasa kan yakar cutar Coronavirus da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Ya yi kira ga maaikatan lafiya su kula da kansu wajen jinyar marasa lafiya.

Shugaban Kwamitin, Boss Mustapha, ya ce yadda masu cutar ke karuwa a jihar Kano na ci gaba da tada musu hankali.

Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da hakan a Abuja a yayin jawabi ga kwamitin.

Ya ce: “Halin da jihar Kano ke ciki abin tada hankali ne. Kwamitin na ci gaba da aiki tare da gwamnatin jihar don shawo kan lamarin.

“Kwamitin ya gano cewa ana ci gaba da samun masu cutar a kasar nan. Wannan kuwa ya danganta ne da yadda aka fadada wuraren gwajin.”

Mustapha ya kara da cewa, ganin yadda lamarin ya sake yawaita, sun sauya sabbin tsarin gwaji don yanzu gida-gida ake bi don yin gwajin a jihohin Legas da Abuja.

Kamar yadda yace, gwaji, tantancewa, killacewa da kula da masu cutar ya zama dole in har ana bukatar takaita yawan masu kamuwa da cutar.

Ya mika godiyarsa ga sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta addinin musulunci a kasar nan a kan kwamitin fatawa ta gaggawa da ya kafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here