Mun Garzaya Jihar Kano Domin Kada Ta Zamo Cibiyar Cutar – FG

0
344

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN tarayya ta ce ta koma jihar Kano don ba da dauki gudun kada jihar ta zama wata cibiya ta yaduwar muguwar annobar.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da annobar, Boss Mustapha, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a yayin jawabi ga manema labarai.

Sakataren gwamnatin tarayyar ya umarci hukumar kula da cututtuka masu yaduwa (NCDC) da ta garzaya Kano tare da hada gwiwa da gwamnatin jihar don fara zakulo duk wadanda suka yi mu’amala da masu cutar.

Ya nuna damuwarsa a kan yadda cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu suka ki bin umarnin gwamnatin tarayyar na cewa su daina tantance masu dauke da kwayar cutar ko basu magani.

Ma’aikatar lafiya ta tarayya ta tabbatar da cewa hakan na da matukar hatsari ga jama’a baki daya.

A kan halin da Kano ke ciki, Mustapha ya ce:
“Halin da Kano ke ciki har yanzu muna bincike ne tare da dubanshi da kyau.

“Bayan kammala binciken farko, PTF ta umarci NCDC da ta tura kungiyarta don fara daukar matakan da suka dace tare da hadin guiwar gwamnatin jihar.

“Hakan ne kadai zai tsayar da yaduwar muguwar annobar tare da guje wa jihar ta zama sabuwar cibiyar annobar.”

A yayin tsokaci game da rashin biyayyar asibitocin kudi na jihar, ya ce: “PTF ta lura cewa wasu daga cikin cibiyoyin lafiyar jihar na kudi basu bin umurnin gwamnatin na guje wa duba masu cutar.

“Yanayin hatsarin cutar ne ya sa ake gudun yaduwarta ta cibiyoyin lafiya masu zaman kansu. Da yawansu ba su da kayayyakin aikin kula da masu cutar.”

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi kokarin gujewa samun muguwar cutar don tana da matukar hatsarin gaske.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here