Gwamnatin Filato Za Ta Mayar Da Almajirai Zuwa Jihohinsu Na Asali

0
469

 Isah Ahmed Daga  Jos

GWAMNAN Jihar Filato Simon Lalong ya bayyana cewa gwamnatin Jihar za ta kwashe almajiran da ke zaune a jihar, ta mayar da su zuwa jihohinsu na asali. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga al’ummar Jihar, ta gidajen rediyo da tilbijin, kan cikar wa’adin makonni biyu na dokar hana fita da aka sanya a jihar, a yammacin ranar Alhamis din nan da ta gabata

Gwamnan ya ce gwamnatin ta dauki wannan mataki, na kwashe almajiran zuwa jihohinsu ne sakamakon halin da ake ciki, na annobar cutar korona wanda babbar barazana ce, ga almajiran.

Ya ce sun yanke shawarar mayar da almajiran zuwa jihohinsu na asali ne, a taron  kungiyar su ta Gwamnonin arewa.

Ya ce tuni gwamnatin jihar ta Filato ta kafa kwamiti, na musamman karkashin jagoranci Mai ritaya Birgediya Janar  Salihu Inusa, da zai gudanar da wannan aiki.

Gwamnan ya yi bayanin cewa sakamakon cikar wa’adin makonni biyu, na dokar hana fita da aka kafa a jihar. Gwamnatin jihar ta sake daga wannan doka zuwa ranar Litinin mai zuwa, inda dokar za ta ci gaba da aiki.

Gwamnan ya ce a makonni biyu da aka yi da wannan doka, an binciki mutane 231 da ake zargin suna dauke da wannan cuta,   inda aka killace mutane 221 da suka shigo jihar, daga jihohin da wannan cuta ta bulla.

Ya ce a  duk binciken da suka yi, har ya zuwa wannan lokaci ba su gano wani da yake dauke da wannan cuta ba, a jihar.

 Ya ce a yayin da ake dokar hana fitar, Kotunan tafi da gidanka na musamman da gwamnatin jihar ta kafa, don hukunta wadanda suka karya wannan doka, sun hukumta mutane  1,607 da suka karya wannan doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here