Gwamnonin Najeriya Su 36 Sun Yi Kira Ga Shugaba Buhari A Sassauta Dokar Hana Zirga-zirga….

0
285

Kungiyar gwamnoni ta Najeriya

Rahoton Z A Sada

GWAMNONIN jihohin Najeriya sun bukaci shugaba Muhammadu Buhari, da ya amince a wajabta wa jama’a amfani da takunkumin fuska a duk fadin kasar.

Wannan kira ya biyo bayan fargabar da ake da ita na karuwar masu cutar korona a kasar, kamar yadda gwamnonin suka rubuta a cikin wata wasika.

Gwamnonin su 36 na ganin cewa akwai bukatar shugaban kasar ya amince da wannan bukata tasu.

Wasikar ta kungiyar gwamnonin ta ce ”ya kamata a wajabta wa kowa da kowa amfani da takunkumin fuska kama daga matakin gwamnatin tarayya zuwa na jihohi domin dakile yaduwar cutar ta korona”.

Har yanzu dai fadar shugaban kasar ba ta ce komai ba a kan ko Buharin ya samu wasikar sannan ko akwai yiwuwar shugaban kasar ya dauki wannan shawarar.

Wasu majiyoyi biyu daga fadar shugaban kasar sun ce kamar an rubuta wasikar ne da nufin shawara ga kwamitin ko-ta-kwana da shugaban kasar ya kafa.

Sun ce kwamitin zai yi wa shugaban kasar karin bayani a game da shawarar da kungiyar gwamnoni ta bayar a ranar Lahadi.

A bangare guda kuma, kungiyar gwamnonin ta bukaci shugaba Buharin da ya yi gyara a dokar hana fitar da ya sanya a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja, babban birnin kasar.

Kungiyar ta ce, yakamata a dan sassauta dokar, sannan kuma a hana zirga-zirga a tsakanin jihohi gami da hana gudanar da taruka.

Kungiyar gwamnoni ta ce idan aka ci gaba da aiwatar da dokar hana fitar, to ya kamata a rinka barin kayayyakin abinci da na kula da lafiya da man fetur da dai makamantansu.

A yanzu haka dai wato a ranar Asabar 26 ga watan Afirilu, 2020, akwai sabbin mutum 87 da suka kamu da cutar korona a kasar abin da ya kawo adadinsu 1182.

Sai kuma wadanda suka mutu sakamakon cutr 35, inda 222 kuma suka warke daga cutar.

Jihar Legas ce dai ke da adadi mafi yawa na masu wannan cuta ta korona a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here