Sarkin Kano Ya Yi Magana Kan Yawaitar Mutuwar Jama’a A Masarautarsa

0
451

Daga Usman Nasidi

MAI martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya tabbatar da cewa ba annobar covid-19 ce ke hallaka mutane a masarautarsa ba, kamar yadda wasu suke zargi.

A cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi, Sarkin ya ce ma’aikatar lafiya ta jiha ta sanar da fadarsa cewa asarar dumbin rayukan da ake yi, ba sanadiyyar barkewar annobar cutar covid-19 bane.

Ya yi addu’ar Allah ya ji kan wa danda su ka mutu tare da yi wa marasa lafiya fatan samun sauki.

Da ya ke magana a kan annobar cutar covid-19, sarki Aminu ya yi kira ga mazauna Kano da su yi aiki da shawarwarin da hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa ta kasa (NCDC) ta bayar a kan dakilye yaduwar covid-19.

Bayan ya yi sallama ga jama’a, sarki Aminu ya ce; “mu na son sanar da jama’a cewa ma’aikatar lafiya ta aiko mana da rahoto a kan yanayin da ake ciki dangane da barkewar annobar covid-19 a jihar Kano.

“Rahoton yana da matukar muhimmanci, saboda ya tabbatar mana da cewa cutar covid-19 gaskiya ce tunda ga shi an tabbatar da samun mutane 73 ma su dauke da ita a Kano.

“A dangane da haka, ya zama wajibi garemu mu yi muku tuni a kan muhimmancin bin shawarwarin masana da kwararru a bangaren kiwon lafiya.

“Ku guji wurare ma su cunkoson jama, a ke amfani da takunkumi tare da yawaita wanke hannu da sabulu.

“Mu na kira gareku da ku daina kyarar wadanda annobar cutar ta harba, a guji yada labaran karya da kan iya firgita jama’a.

“Ina kira gareku da ku saka ido a kan ‘ya’yanku don tabbatar da cewa basu cigaba da buga kwallo a cikin lunguna ba.

“Kazalika, ma’aikatar lafiya ta ba mu tabbacin cewa ba annobar cutar covid-19 ce ke hallaka mutane a Kano ba.

“Ina mika sakon ta’aziyya ga iyalan duk wanda su ka rasa wani nasu, ina kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu tare da cigaba da neman taimakon Allah.

“Marasa lafiya Allah basu lafiya, Allah ya cigaba da karemu, ya ba mu zaman lafiya da yalwar arziki, ” a cewar jawabin sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here