Ya Kamata A Bude Kasuwanni, A Yi Taka-Tsantsan – Masana Ga Gwamnatin Tarayya

0
372

Daga Usman Nasidi.

MASANA sun fara yin kira ga gwamnatin tarayya ta saki hanyoyi, ta bude kasuwanni a Najeriya. Makonni hudu kenan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa dokar hana fita.

Atedo Peterside da majalisarsa ta kwararru da ke nazari a kan annobar COVID-19, sun bukaci gwamnatocin jihohi da na tarayya a Najeriya su bude kasuwannin da ke fadin kasar.

Shugabannin gidauniyar nan ta Anap Foundation COVID-19 Think Tank su ne su ka bayyana wannan matsaya a wata takarda da su ka fitar.

Atedo Peterside da Dakta Abubakar Siddique Mohammed wanda su ne shugabannin wannan gidauniya da aka kafa a ranar 22 ga watan Afrilun 2020 su ka sa hannu a takardar.

Wannan gidauniya ta na dauke da mutane 18 da aka zakulo daga kowane yankin Najeriya. An kuma zakulo wasu ‘yan kungiyar daga kasashen waje irinsu Jamus da kasar Amurka.

Kungiyar Peterside ta ce Gwamnatin tarayya ta bude hanyoyi
Wadannan gungun masana sun ce sun gano jami’an tsaro su na kashe Bayin Allah kamar
yadda annobar COVID-19 ta ke yi. Wannan ya sa masanan su ke ganin ya kamata ayi gyara.

Jawabin ya ce: “ Lokaci ya yi da za a sake duba matakin nan, domin ta tabbata cewa garkame mutane a gida da aka yi ba ya aiki. Abinci ya kara tsada a mafi yawan garuruwan birni.”

“Kudin mota ya kara kudi saboda matsalar rashin tsaro, da kuma rufe iyakokin jihohi da ake cewa an yi, tare da matsalar da aka samu na rashin kayan bukata a kasuwa. ” Inji kungiyar.

Wadannan masana sun kuma fadawa gwamnati cewa takaita ranakun shiga kasuwani ya jawo cunkoso na babu gaira babu dalili, wanda hakan ya sa mutane ba su bin dokar tazara.

A karshe, masanan sun bada shawarar a daina samun cincirindon, sannan a dakatar da taron addini, tare da cigaba da rufe makarantu, amma a bar wadanda za su iya fita su je aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here