‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Taron Ma Su Zaman Makoki A Kaduna

0
334
IGP na 'yan sandan Najeriya

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WASU jami’an yan sanda sun tarwatsa dandazon mutane da suka halarci zaman makokin wani matashi a jahar Kaduna.

An gudanar da zaman makokin ne a ranar Asabar a garin Maraban Rido da ke karamar hukumar Chikun na jahar.

Yayin da suke tarwatsa taron, jami’an tsaron sun kama mutane da dama kan karya dokar hana fita da gwamnatin jahar ta kafa.

Gwamnatin jahar ta haramta duk wani taro na jama’a, ciki harda na zaman makoki da bukukuwa a kokarinta na hana yaduwar Coronavirus a jahar.

Ta kuma yi umurnin rufe jahar a ranar 26 ga watan Maris, har sai baba ya gani.

Ciki harda hana zinga-zirga, da haramta tafiye-tafiye da taron jama’a.

An kama mutanen ne yayin da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida a Kaduna, Samuel Aruwan, ya fita rangadi a wasu yankunan jahar.

Aruwan, wanda ya samu rakiyan wasu shugabannin hukumomin tsaro, ya yi bayanin cewa sun fita rangadi ne don ganin yadda ake bin dokar da gwamnati ta saka.”

Kwamishinan yan sandan jahar, Umar Muri, wanda ya kasance cikin tawagar gani da idon, ya yi magana da manema labarai.

Ya bayyana cewa zaman makokin ya sabawa umarnun gwamnati da ta hana taron jama’a.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here