Gwamnatin Tarayya Ta Yi Watsi Da Kano Kan Yakar Korona – Ganduje

0
381

Rahoton Z A Sada

GWAMNAN jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya ce kwamitin da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar korona a kasar ya yi watsi da jihar Kano duk da mawuyacin halin da jihar ta shiga.

A wata hira da ya yi da wakillin BBC, Gwamna Ganduje ya ce lamarin da ake ciki a Kano yana da ban tsoro.

“Halin da ake ciki yanzu, wato muna da babbar matsala, kuma zan iya cewa da kai wannan hali a yanzu haka dai gaskiya ba shi da kyau kuma abin tsoro ne,” in ji Ganduje.

Ya ce babban abin da aka dogara da shi a kokarin dakile Korona a jihar shi ne gwaji, wanda ya ce an shafe kwanaki biyar zuwa shida wadanda aka dauki samufurinsu ba su san matsayinsu ba.

“Kayan da ma ake daukan (samfurin) a kai Abuja sun yi karanci, kuma ba kaya ne wanda gwamnati za ta je kasuwa ta saya ba,” a cewar Ganduje.

Ya kara da cewa “Wadanda aka dau samfurinsu ba su san matsayinsu ba. Za su ci gaba da hulda da mutane.”

Gwamna Ganduje ya ce “Saboda haka wannan babbar matsala ta kwamitin shugaban kasa na Abuja, shi kansa babban daraktar (hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa NCDC ya zo nan Kano ya kwana, to amma tun da ya tafi ba mu sake jin duriyarsa ba.”

To sai dai kwamitin na shugaban kasa kan yaki da cutar korona ya musanata wadannan zarge-zarge, inda ya ce suna bai wa Kano kulawa ta musamman.

“Shi ma minista (na lafiya) ya sani cewa wannan dakin gwaji ba ya aiki, amma ba mu sake jin komai ba,” a cewar Gwamnan.

Gwamna Ganduje ya kara da cewa baya ga karancin cibiyoyin gwaji a Kano, jihar ba ta samun isassun kayan da za a yi gwajin da su wadanda ya ce gwamnatin tarayya ce kadai ke samar da su.

“Wani abin takaicin ma shi ne kwalaben da za a sa wannan (samfurin) babu su isassu, kuma ba za a iya sa wa a cikin wani waje ba idan ba wadannan kwalabe ba,” a cewar Gwamnan na Kano.

Ya ce a gaskiya ba ma samun abin da ya kamata. “Gaskiya ba ma samun taimako da ma hadin kai daga shi wannan kwamitin na gwamnatin tarayya.”

Ganduje ya ce ya yi magana da jami’an gwamnatin tarayya a matakai daban-daban, amma har yanzu babu wani sakamako.

“Na yi magana da sakataren gwamnati, na yi magana da mataimakin shugaban kasa da kuma wasu mukarrabai, kamar shi minista na kiwon lafiya, na yi magana da su”

Gwamna Ganduje ya ce amsar da yake samu ita ce za a yi wani abu a kai, “amma har yanzu ban ga komai a kai ba,”in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here