Kwankwanso Ya Rubuta Wa Buhari Wasika Kan Mace-macen Kano

0
438
Wani taro na 'yan Kwankwasiya

Rahoton Z A Sada

TSOHON Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwanso ya rubuta wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wasika kan yawan mace-macen da ke faruwa a Kano.

Sanata Kwankwaso ya bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar mataki domin ceto rayukan al’umma.

A cikin wasikar da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon Gwamnan ya ce ya rubuta wasikar ne saboda a cewarsa abin da ke faruwa a Kano abin tsoro ne musamman yadda mutane ke mutuwa kusan a kullum tun bayan soma yaki da cutar korona a jihar da kuma hana mutane fita.

A makon da ya gabata ne tsohon Gwamnan jihar Kano din ya bayar da gudunmuwar asibiti ga gwamnatin abokin hamayyarsa Abdullahi Umar Ganduje don jinyar masu fama da cutar korona.

Kwankwaso ya ce “wannan gini an tanade shi ne domin amfanin mambobinmu na Kwankwasiyya da ma dukkan dan jihar Kano.

“Kuma bayan kammala shi mun shigo da kayan aiki, sai ga wannan ciwo ya shigo. Shi ya sa muka sayo kayyakin yaki da korona.

”Akwai ma wasu karin wurare kamar dakunanmu na taro da idan bukatar bayar da su ta taso to za mu bayar da su. Amma muna fata Allah ya takaita.”

A ‘yan kwanakin nan ana samun karuwar mace-macen jama’a a jihar Kano, abin da ya tayar da hankalin al’umma.

Masu gadin makabartu daban-daban da aka ta ji ta bakinsu sun tabbatar da cewa sun ga karuwar wadanda ake binnewa fiye da kowane lokaci a baya.

Wasu na ganin annobar cutar korona ce take yi wa mutane dauki dai-dai, sai dai gwamnatin ba ta tabbatar da hakan ba.

Sai dai kuma a yanzu haka an shafe kwanaki ba tare da an yi gwajin cutar ba a Kano saboda rashin kayan aiki.

A ranar Litinin ma gwamnatin jihar ta sanar da mutuwar karin mutum biyu da cutar korona ta kashe a jihar.

Yanzu mutum uku kenan cutar korona ta kashe a jihar, kamar yadda ma’aikatar lafiya a jihar ta sanar a shafinta na Twitter.

Sai dai alkalumman yawan wadanda suka kamu da cutar korona ba su sauya ba daga mutum 77 da hukumar yaki da cutuka masu yaduwa a kasar ta sanar ranar Lahadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here