Ba Za Mu Yarda A Zaftare Albashin Ma’aikata Da Sunan Coronavirus Ba – NLC

0
371

Daga Usman Nasidi.

KUNGIYAR kwadago ta Najeriya, NLC ya gargadi gwamnati da ma’aikatu game da dakatar da albashin ma’aikata da sunan annobar Coronavirus, ko kuma zaftare musu albashi.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba ne ya sanar da haka a ranar Talata cikin wata sanarwa da ya fitar don tunawa da ranar ma’aikata da ta duniya na shekarar 2020.

Wabba ya yi kira ga NLC na kowace jaha da ta yi tirjiya ga duk wani yunkurin gwamnati da ma’aikatu na zaftare albashin ma’aikata, saboda a cewarsa ba yanzu ba ne lokacin rage albashi ba.

“Muna tabbatar ma ma’aikata cewa babban abin da muka sa a gaba shi ne farfado da tattalin arziki domin su koma bakin aikinsu, mun mayar da hankulanmu ga inganta albashin ma’aikata, dawo da ma’aikatan da suka rasa ayyukansu.” Inji shi.

Sai dai Wabba yace duba da halin da ake ciki na annobar Coronavirus, ba za a gudanar da bikin tunawa da ranar ma’aikata kamar yadda aka saba ba.

“Za mu samar da hanyoyin da ma’aikatan Najeriya za su samu sakon mu na shekarar 2020, muna kira ga ma’aikata su tuntubi babban ofishin NLC idan har aka musu wani rashin adalci da ya shafi COVID-19.

“Yayin da muke sa ran ganin karshen wannan ibtila’i, ya dace mu ci gaba da kula, mu zauna a gida , kuma mu kasance cikin aminci.” Inji shi.

A yanzu haka ma’aikatu masu zaman kansu sun aika ma’aikatansu hutu ba tare da biyansu albashin ko sisi ba, yayin da wasu kuma suka rage albashin ma’aikatan nasu.

Kwalejin horas da matuka jirgin sama dake garin Ilorin ta sanar da rage kashi 10-42 na albashin ma’aikatanta na watan Afirlu, amma ban da masu amsan N80,000 kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here