Covid-19: Hukumar NEDC Ta Bai Wa Jihar Yobe Gudunmawar Kayayyakin Aiki

0
467
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
HUKUMAR sake farfado da ci gaban arewa maso gabas (NEDC) ta ba gwamnatin jihar Yobe gudunmawar motocin daukar majinyata guda biyu, kayan abinci da magunguna na miliyoyin naira, a kokarinta na yaki da yaduwar cutar Korona.
Manajan Darakta a hukumar NEDC, Alhaji Goni Alkali shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da gudumawar ga shugaban kwamitin yaki da yaduwar cutar a jihar Yobe, kuma mataimakin gwamnan jihar, Idi Barde Gubana a Damaturu.
Daraktan, wanda Daraktan mulki da kudi a hukumar ya wakilta, Alhaji Muhammad Jawa Gashua, ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa hukumar ta
bai wa gwamnatin jihar Yobe wannan gudumawar shi ne bisa ingantaccen shirin da ta yi na dakile yaduwar cutar a fadin jihar tare da gamsuwa da tsarin kiwon lafiya a jihar.
Haka kuma, ya kara da cewa baki dayan jihohi shida dake wannan shiyya ta arewa maso gabas sun ci gajiyar irin wannan gudumawar.

Da yake jawabi lokacin da yake karbar kayayyajin tallafin, mataimakin gwamnan jihar Yobe, kuma shugaban kwamitin yaki da cutar korona
Alhaji Idi Barde Gubana ya yaba da wannan kokari na hukumar NEDC dangane da gudumawar tare da alwashin raba kayan kamar yadda ya dace.
Wasu daga cikin kayayyakin abincin sun hada da shinkafa, masara, man girki da sauran su,
kana sai kuma kayan magunguna wadanda su ka kunshi rigunan kariya, na’urorin da ke taimakawa majinyata shakar iska guda biyu, safar roba ta hannu da makamantansu..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here