Gwamnatin Yobe Za Ta Rarraba Kayayyakin Abinci Ga Masu Karamin Karfi Kimanin Dubu 20.

0
350
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
A ranar Alhamis, Hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Yobe (SEMA), ta bayyana cewa za ta raba kayyakin abinci ga magidanta kimanin 20,000 a daukwacin kananan hukumomin 17 a jihar.
Babban sakataren hukumar, a jihar Yobe, Dakta Muhammed Goje, shi ne ya tabbatar da hakan, a lokacin gudanar da aikin tura kayan abincin zuwa
kananan hukumimi daban-daban, a birnin Damaturu.

“Wannan daya ne daga cikin muhimin yunkurin da Gwamna Mai Mala Buni ke yi a kowane lokaci. Kuma kamar yadda kowa ya sani, muna aiwatar da irin wannan aikin raba kayan abincin lokaci bayan lokaci, wanda talkafin zai shiga kowane lungu da sakon zuwa hannun masu karamin karfi a daidai lokacin da ake fuskantar azumin ramadan”.

“Sannan kuma, ta dalilin yadda duniya ke fuskantar kalubalen kwayar Korona, wanda hakan ya sanya Gwamna Buni ya bayar da umurnin a raba wa magidanta kimanin 20,000 kayan abinci a kananan hukumomi 17 da ke fadin jihar Yobe”.

Bugu da kari kuma, Dakta Goje ya kara da cewa, sun kafa kwamitin da zai kula da raba kayan a daukwacin kananan hukumomi 17 da ke jihar, wadanda su ka kunshi masu ruwa da tsaki domin raba kayan abincin ga masu karamin karfi
a cikin al’umma”.

Ya kara da cewa, yanayin karamin karfin ya danganta da halin da mutum yatsinci kan shi a rayuwa, kana da matsalolin da su ka shafi yankin da
mutumin ya ke, kuma manufar tallafin shi ne don rage wa jama’a radadin yanayin da mu ke ciki a lokacin garkame garuruwa, a matsayin hanyar dakile yaduwar annobar cutar korona.
Haka kuma ya ankarar da cewa, hukumar SEMA za ta raba kimanin buhunan shinkafa 21,000 da sauran kayan masarufi, irin su man girki, tumatir da
makamantan su, hadi da bayar kulawa ta musamman ga marayu da gidajen marasa shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here