‘Yan Bindiga Sun Kai Harin Kwantan Bauna, Sun Kashe 1, Saura Sun Jikkata A Kaduna

0
632

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

WASU gungun miyagu ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in rundunar ‘yan sandan Najeriya mai mukamin Insifekta a garin Falwaya dake kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

‘Yan bindigan sun kai harin kwantan bauna ne a kan wata motar ‘yan sanda da ke tafiya da yammacin Litinin, 27 ga watan Afrilu a kan hanyarsu ta zuwa Birnin Gwari.

Wani dan banga da ke yankin, Hussaini Imam ya shaida cewa jami’in dan sandan da aka kashe yana aiki ne a ofishin ‘yan sanda da ke Buruku, cikin karamar hukumar Chikun.

Hussaini ya ce ‘yan bindigan sun sake kai wani samame a kauyen Udawa dake karamar hukumar Chikun a ranar Talata, inda suka yi awon gaba da dakacin kauyen.

“Bayan sun kashe Sufeta Dantani, tare da jikkata abokan aikinsa a ranar Litinin, ‘yan bindigan sun karasa zuwa wani kauyen Udawa inda suka yi awon gaba da Dagacin kauyen tare da wasu mutane 5, sa’anann suka kashe wani mutum mai suna Lado” Inji shi.

Ko da majiyar mu ta tuntubi Rundunar ‘yan sandan jahar, sai Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mohammed Jalige ya ce bai samu labarin harin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here