Farashin Kayayyakin Masarufi Ya Tashi Sama Sakamakon Dokar Hana Fita Da Zuwan Azumi

  0
  606
  Alhaji Ibrahim Baban Kanwa Hassan

  Isah Ahmed Daga Jos

  A yayin da al’ummar musulmin Najeriya da sauran kasashen duniya  suka fara Azumin watan Ramadan, a makon da ya gabata,farashin kayayyakin masarufin da al’ummar musulmi suke amfani da shi, a lokacin watan Azumin Ramadan, kamar  suga da madara da shinkafa da dai sauransu, sun ya yi tashin gwauron zabo.

  A binciken da wakilinmu ya gudanar a babbar kasuwar sayar da kayayyakin masarufi ta ‘Yan kwalli da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato. Kasuwar da ta yi suna wajen sayar da kayayyakin masarufi, a yankin Arewa ta tsakiya ya gano cewa farashin kayayyakin masarufin ya yi tashi sama sosai.

  Wakilinnamu ya gano cewa buhun suga da ake sayarwa kan farashin N12,000  makonni biyu da suka gabata,  yanzu ana sayar da shi kan kudi  N24,000. Har’ila yau buhun madara da ake sayar kan farashin  N27,000 makonnin hudu da suka gabata, yanzu  ya kai N47,000.  Shinkafa ‘yar gida a da ana sayar da buhu kan N17,000 yanzu ta kai  N20,000. Shinkafa ‘yar waje a da ana sayar da buhu N18,000 amma yanzu ta kai N23,000.

  Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan al’amari, shugaban kasuwar ta ‘yan kwalli Alhaji Ibrahim Baban Kanwa Hassan ya bayyana cewa,  abubuwan da suka kawo tashin farashin kayayyakin masarufi a wannan lokaci suna da yawa, amma babban abin da ya rufe komai shi ne maganar annobar korona.

  Ya ce maganar wannan annoba  kan harkokin  kasuwanci duk duniya ne, domin wasu kayayyakin da ake fita da su waje,  darajarsu ta fadi kamar man fetur,  don haka harkoki ba sa tafiya, kamar yadda ya kamata.

  Ya ce a wannan kasuwa a shekarun baya,  dai dai  wannan lokaci suna iyakar kokarinsu, wajen zama da ‘yan kasuwa, suna rokonsu kan su rika dubawa kan kada tashin farashin kayayyakin ya rika zuwa daga wajensu.

  Ya ce don haka a shekarar da ta gabata, ba a sami tashin farashin kayayyakin masarufi ba, a wannan kasuwa a lokacin watan Azumin.

  ‘’Amma a bana da abin ya zo ya hadu da wannan annoba . Kuma ga kayan ba sa samuwa yadda ya kamata sakamakon wannan annoba, domin ko ka sayo kayan kafin ya zo, wani jidali ne saboda gamuwa da jami’an tsaro a hanya, da suke karbar kudade kafin su bari a wuce, duk idan aka hada wadannan dawainiya, suna hawa kan kayan ne. Wannan shi ne abin da yake faruwa’’.

  Alhaji Ibrahim Baban Kanwa ya yi bayanin cewa babu shakka akwai ‘yan kasuwar da sun ji farashin kaya ya tashi, suna kara farashin kayansu.

  Ya ce amma shi dan kasuwa a kullum abin da yake kula, shi ne idan ya sayar da kayansa ya je ya sayo wani kayan mai yawa, kamar wanda ya sayar. Sau tari idan aka sami tashin farashin kaya, karshe xan kasuwa ya kan sami raguwar yawan kayan da yake sayarwa.

  Ya ce idan aka cigaba da haka, sai kaga an cire dan kasuwar domin zai dawo babu kayan, don haka ‘yan kasuwa suna duba wannan al’amari.

  Ya ce  kullum kamfanoni  ne suke zuwa su kara farashin kayayyakinsu, da hujjar cewa dala ta tashi. Don haka ya kamata gwamnati ta riqa sanya ido, kan yadda kamfanoni suke sanya farashin kayayyakin da suke yi.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here