Gobara Ta Lamushe Shaguna Masu Yawa A Garin Kaduna

0
334

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

AKALLA shaguna 20 wadanda suka hada da wurin siyar da magani ne suka babbake a jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne wurin karfe 7 na yamma a wurin Constitution road da ke babban birnin jihar  wanda ba a san dalilin tashin gobarar ba a lokacin da mukaje dauko rahoton.

A yayin da aka dauko wannan rahoton, jami’an hukumar kwana-kwana da sauran masu taimakon gaggawa duk basu isa wurin ba.

Amma kuma, mazauna yankin tare da masu wucewa ne ke kokarin kashe gobarar.

Hakazalika, babu daya daga cikin masu shagunan da ke kusa saboda dokar hana zirga-zirgar da gwamnatin jihar ta saka don yaki da cutar COVID-19.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here