Rishi Kapoor: Shahararren Tauraron Bollywood Ya Mutu

0
419
Marigayi Rishi KapoorMarigayi Rishi Kapoor yana wani jawabi a wajen wani taro na Fim

Rahoton Z A Sada

KWANA daya bayan mutuwar fitaccen dan wasan fim Irrfan Khan, mun sami rahoton mutuwar Rishi Kapoor bayan ya shafe shekaru biyu yana jinyar cutar kansa.

Rishi Kapoor mai shekara 67 ya mutu ne a asibitin Sir HN Reliance Foundation da ke birnin Mumbai na kasar Indiya.

Matarsa ​ Neetu Kapoor ce ke jinyarsa yayin da rai yayi halinsa, kuma dan uwansa ​​Randhir Kapoor ne ya sanar da rasuwar tasa.

Shahararren tauraron fim, Amitabh Bachchan ya bayyana cewa mutuwar ta girgiza shi matuka, cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter:

“Rishi Kapoor .. ya tafi .. ya yi gaba .. Na kasance halakakke!.”

A shekarar 2018, Rishi Kapoor ya kamu da cutar kansa, wanda hakan ya sa ya tafi birnin New York na tsawon fiye da shekara guda don karbar magani.

Amma ya dawo Indiya a watan Satumba na 2019 bayan ya murmure.

Rishi Kapoor shi ne ɗan marigayi tauraron fim Raj Kapoor kuma yana da ‘yan uwansa ​​Randhir, da Ritu Nanda da Rima Jain da kuma Rajeev Kapoor.

Ya yi fim dinsa na farko Bobby tare da Dimple Kapadia a 1973 kuma an gan shi a matsayin mai wasan kwaikwayo na yara a fina-finai kamar Shree 420 da Mera Naam Joker.

Ya kasance cikin fina-finan masu farin jini da aka fitar kamar Amar Akbar Anthony, Laila Majnu, Rafoo Chakkar, Sargam, Karz, Bol Radha Bol da sauransu.

Ya kuma fito a wasu fina-finai Kapoor and Sons, D-Day, Mulk da 102 Not Out.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here