Ya Kamata Cutar Korona Ta Zama Babban Darasi Ga Shugabannin Najeriya-Imam Usama

  0
  492

  Isah Ahmed Daga Jos

  IMAM Ibrahim Awwal [Usama] shi ne  Limamin masallacin gidajen ‘yan majalisar tarayya da ke  zone B, Apo babban birnin tarayya Abuja. A  wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu kan annobar cutar korona, ya bayyana cewa ya kamata wannan cuta ta zama babban darasi ga shugabannin Najeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK: Mene ne za ka ce dangane da abubuwan da suke faruwa kan cutar annobar korona, musamman a nan Najeriya?

  Imam Usama: Na farko sai mu godewa Allah kan jarrabawa da yayi mana, ta wannan annoba ta Kurona. Dama haka Allah yake kawo jarrabawa ta bala’a, don ya zama natsuwa ga mumunai. Kuma a cikin wannan annoba  akwai karantarwa a ciki  kuma wata  babbar ishara ce  ga shugabannin Najeriya.

  Domin a da idan muka lura idan mutum ya fita kasar waje ya dawo, za aga idan yana da mata biyu, kowace daga cikin matan, tana kokari ace a dakinta ya sauka, domin ta bude kayan  tsarabar da ya dawo da shi. Amma yanzu sakamakon wannan annoba, idan mutum ya je kasar waje yana dawowa, matarsa da ‘ya’yansa da yaran gidansa, kowa yana gudunsa. Saboda gudun kada su kamu da wannan cuta.

  Haka kuma ada idan muka    lura manyan kasar nan,  sun dauka cewa idan ba su da lafiya, idan ba sun je Ingila ko Amerika ko Rasha ko wata kasar Turai ba, ba za su sami maganin cutar da take damunsa ba.

  To a wannan karon, da Allah ya tashi sai ya fito da  wannan cuta, daga wadannan kasashe da suke zuwa neman maganai. Kuma sai suka gudo suka dawo Najeriya, ga shi wasu wannan cuta ta riga ta kama su.

  Yanzu tun da ya zamanto babu wurin da za su je su yi wannan magana a waje,  ya kamata wannan annoba, ta zama darasi gare su.

  Yanzu manya kowa tsoran wannan annoba yake yi, sun koma gida sun kulle, wasu ko sallah ba sa iya fitowa su yi. Musamman daga lokacin da tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarrayyar Abba Kyari ya rasu.

  Muna fatar nan gaba, idan Allah ya sa muka fita daga wannan annoba,  su gane  su tsaya su yi abubuwan da suka kamata. Wajen ingnata asibitocin Najeriya, ta hanyar  samar masu da kayayyakin aiki irin na zamani.

  Har’ila yau muna fatar shugabannin Najeriya, da suka fita waje suka ajiye kudadensu ko suka kafa kamfanoni su gane cewa idan ba a yi sa’a ba, wata rana za su iya rasa wadannan kudade, ko kamfanonin. Don haka ya kamata su dawo da wadannan dukiyoyi, zuwa gida domin amfanin kansu da al’ummar Najeriya baki daya.

  GTK: Mutane suna ta koke-koke  cewa har ya zuwa yanzu, ba su ga tallafin da gwamnati ta ce za ta bayar ba, kan wannan annoba, mene ne za ka ce?

  Imam Usama:  Idan ka lura za ka ga akwai tallafi da wasu kasashe  suke yi wa al’ummominsu,   saboda wannan hali da aka shiga. Amma gaskiya  har yanzu ban ji gwamnatin Najeriya, ta kawo wa talakawa wani tallafi ba, kan wannan annoba. Duk da cewa tun da wannan annoba ta zo Najeriya, gwamnati  ta yi ta cewa za a bai wa mutane tallafi, amma har yanzu an rasa ina wannan tallafi ya tafi.

  Ya kamata shugabanni da sauran al’umma  su gyara halayensu, sakamakon wannan annoba,  amma wani abin mamaki maimakon shugabanni da mutane su gyara halayensu,  su tausaya,  sai ga shi ana zargin kudaden da aka bayar na tallafi  wasu suna karkatar da su. Wasu ma  ana zargin suna ta kokarin cutar ta isa, wajensu saboda abin da za su samu na wannan  tallafi. Wannan al’amari abin takaici ne.

  GTK: To, mene ne za ka ce kan matakan da aka dauka na magance yaduwar wannan cuta musamman wajen rufe garuruwa da wuraren ibada?

  Imam Usama: Gaskiya  an yi sakaci, domin tun da farkon   bullar wannan cuta  a wasu kasashe, ya kamata  an hana  shigowa Najeriya,  a kulle dukkan filayen jiragen saman Najeriya. Amma sai aka yi sakaci,  sai da wasu suka shigo da wannan cuta, sannan aka rufe. Da tun da farko an kulle kasar nan,  da haka bata faru ba.

  Yanzu kuma  a ce an kulle wannan gari, gobe a ce an kulle wancan gari , duk wannan ba shi da wani tasiri. Domin zirga-zirga, ana yi ba a fasa ba.

  Sannna kuma kamar maganar kulle masallatai da aka yi. A Najeriya an yi annoba iri daban daban, amma a  ba taba annobar da ta sanya aka  kulle masallatai ba. Har yanzu ba za ka iya nuna mutum 40, da suka mutu  sakamakon wannan cuta ba.

  Idan ka dauki mutanen da  zazzabin typod da maleriya yake kashewa a Najeriya, suna da yawa. Amma saboda wannan cuta duniya an  yaya ta a duniya, aka dauki irin wadannan, matakai wadanda basu dace ba.

  GTK: To, a ganinka mene ne mafita kan wannan al’amari?

  Imam Usama: Na daya  gwamnati taji tsoran Allah ta kalli halin da talakawan kasar nan suke ciki,  a wannan lokaci. Tun kafin kulle mutane a gidajensu,  akwai mutane da dama, da idan suka fita da kyar suke iya samun abin da za su ci. Saboda halin matsin  da aka shiga a kasar nan.

  Yanzu kuma aka zo aka ce an yi dokar kulle, kada kowa ya fito. An ce mutane su zauna a gida, ba ka ba su tallafin da ka ce za ka bayar ba.  Yakamata tun kafin a yi dokar nan, a yi wani tsari na tallafa wa mutane da abin da za su ci.

  Saboda haka nake tausayawa shugaban kasa  duk wani gwamna kan kulle mutanen da suka yi, ba tare da sun ba su abin da za su ci ba. Musamman a wannan wata na Azumin Ramadan. A ce a wannan wata, wani ya wayi gari ya tashi babu abin da zai ci, maye za a fada wa Allah, a ranar tashin alkiyama?.

  Ya kamata gwamnatoci su yi kokari sa tallafa wa al’umma da kayayyakin abinci, a wannan hali na kulle da ake ciki. Kuma su umarci dukkan masu hali, su daure su debi wani yanki na dukiyarsu su tallafa wa al’ummar da suke tare.

  Bayan haka ni a ra’ayina, akwai alherai da a wannan annoba ta Kurona ta kawo. Daga cikin wadannan alherai, akwai  maganar hadin kai, babu maganar  kabilanci ko addini ko siyasa, duk an  taru wannan annoba. Kowa ya koma ana neman mafita kan wannan annoba.

  Haka kuma yanzu idan ka dubi irin mutanen da suka dauki man fetur wani abu. Yanzu man nan ya fadi a kasuwar duniya,  sakamakon wannan annoba.  Ka ga irin wadannan mutane idansu zai fara raina fata, saboda abin da suke gadara da shi darajarsa ta fadi.

  Dole ne suma su koma kan maganar noma da kiwo, kaga wannan ba qaramin alheri bane ga talakawan Najeriya.

  A lokacin da aka rufe kan iyakokin kasar nan, aka ce a daina shigo da shinkafa mutane sun yi ta surutu. Yanzu ga shi an  ga amfanin rufe  iyakokin nan, domin kasashen da ake shigo da shinkafar suma sun kule kasashensu.

  Ka ga da ba a yi noma ba, an dogara da shinkafar waje da mun dada shiga cikin mawuyacin hali. Don haka  ya kamata mu kara rungumar aikin noma, a Najeriya.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here