Yawan Mace-macen Da Ake Yi A Kano Ba Su Da Nasaba Da Covid-19-Inji Al’umar Jihar.

0
692
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
AL’UMAR Jihar Kano sun bayyana cewa mace-macen da ake yawan yi a birnin Kano ba su da nasaba da cutar zamani ta corona virus kamar yadda rahotanni suke ta yaduwa cewa mutane suna mutuwa sanadiyyar kamuwa da al’uma suka yi da ita.
Wakilinmu ya yi wani zagaye domin jin yadda al’uma suka dauki wannan mace-mace da ake yi, inda ya ruwaito cewa dukkanin wadanda suka zanta da Gaskiya Ta Fi Kwabo sun nunar da cewa ko kadan ba cutar corona virus ce take sanadiyyar mutuwar mutane a birnin Kano ba illa zafi da cunkoso da ake samu musamman a wannan lokaci na zaman gida.
Wani mazaunin unguwar Soron dinki Malam Adamu Iliyasu ya ce ” wannan mace-mace da ake samu a birnin Kano zafi da cunkoso ke haddasa su ganin cewa akwai dumbin al’uma cikin kwaryar birnin na Kano duba da yadda yanzu kowa yana zaune a gida babu zuwa ko’ina,sannan kuma dama kuma al’uma suna fama da cututtuka iron su maleriya da zazzabin Taifod wanda duk shekara iron wannan lokaci ake yawan mutuwa”. Inji shi.
Shi ma wani kwararren likita wanda kuma ya bukaci a sakaya sunansa, ya sanar da cewa gaskiya akwai cunkoso a cikin birnin Kano ga shi kuma ana zafi matuka wannan ce ta sanya mutane suke yawan mutuwa kamar yadda abin yake a halin yanzu, sannan ya shawarci gwamnatin jihar Kano da ta sanya idanu sosai kan wannan lamari tareda bullo da hanyoyi na rage cunkoso a unguwanni ta hanyar  kafa garuruwa a sassan birnin jihar  kamar yadda ake gani a kasashen da suka ci gaba.
Idan dai za’a iya tunawa, mutane masu yawa sun rasu cikin makonni biyu a birnin Kano, wanda hakan ta sanya ake kallon lamarin kamar akwai nasaba da cutar nan ta Covid-19, sannan tuni hukumomin jihar ta Kano suka fara daukar matakai na dakile wannan lamari tareda yin bincike don gano dalilai na yawaitar mutuwar da ake yi a jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here