Almajiran Da Aka Kai Kaduna Daga Kano Na Dauke Da Cutar Korona

0
405
Rabo Haladu Daga Kaduna
WASU almajirai biyar da gwamnatin Jihar Kano ta mayar gida zuwa jiharsu ta Kaduna sun kamu da cutar korona, kamar yadda gwamnatin Kaduna ta bayyana a ranar Litinin.
Da wannan adadi, jumillar wadanda ke dauke da cutar yanzu haka a Kaduna sun zama tara.
A wata sanarwa gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Twitter, Kwamishinar Lafiya ta Kaduna Dr Amina Mohammed Baloni ta ce tuni aka kai su asibitin kula da cutuka masu yaduwa da ake killace masu cutar.
Jumillar mutum 15 ne dai suka harbu da korona a Jihar Kaduna ya zuwa yanzu, inda aka sallami shida daga cikinsu, ciki har da Gwamna Nasir El-Rufai.
Kazalika sanawar ta ce yanzu akwai cibiyoyin gwajin cutar guda biyu a Kaduna, daya a birnin Kaduna da kuma daya a Zariya.
A ranar Lahadi ne Gwamna El-Rufai ya tsawaita dokar hana fita a jihar da kwana 30, a yunkurin gwamnatinsa na yaki da yaduwar cutar.
Tun a ranar Laraba ne gwamnonin jihohin arewacin Najeriya 19 suka sanar da rufe dukkanin makarantun tsangaya kuma babu jimawa gwamnatin Kano ta fara mayar da su jihohinsu na asali.
Jihar Kano ta mayar da yaran jihohinsu na asali da suka hada da Katsina da Kaduna.
Akalla yara miliyan tara ne aka yi hasashen za a mayar da su gaban iyayensu sakamakon annobar korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here