Ana Dakon Sakamakon Gwajin Mutuwar Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila

0
490

Rahoton Z A Sada

FADAR masarautar Rano da ke jihar Kano a Najeriya ta ce tana jiran sakamakon gwaji domin tabbatar da ainihin abin da ya yi ajalin sarkinta.

A yammacin Asabar Allah Ya yi wa Sarkin rasuwa a asibitin Nasarawa da ke jihar ta Kano.

Alhaji Tafida Abubakar Il ya rasu ne bayan gajeriyar jinya, yana da shekara 74, kamar yadda Kabiru Alhassan Rurum, dan majalisar tarayya mai wakiltar Rano da Bunkure kuma Turakin Rano ne ya tabbatar wa BBC labarin rasuwar.

Mai magana da yawun Masarautar Ranon Wali Ado ya ce Sarkin ya yi jinyar kwana biyar ne, inda aka kai shi asibiti a ranar Juma’a, sai dai ya ce ana bincike kan abin da ya yi ajalin sarkin.

Kakakin fadar ya ce yanayin mutane da suka kawo gawar mai martaba akwai alamomin da ke nuna akwai matsalar.

”Yanayin Jami’an lafiya da suka kawo gawar da binnewar cikin gaggawa gaskiya ba a saba ganin jana’iza irin hakan ba”

Yana daga cikin sarakuna hudu masu daraja ta daya na sababbin masarautun jihar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya kirkira a bara.

Wali Ado ya ce dama Sarkin yana da cutar hawan jini da ciwon suga da ke taso masa lokaci-lokaci.

Autan Bawo kamar yadda aka fi saninsa ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 17, 12 maza, 5 mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here