Buhari Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar NEMA

0
281

Daga Usman Nasidi.

SHUGABA Muhammadu Buhari ya amince da nadin AVM Muhamadu Alhaji Muhammed (Mai ritaya), a matsayin sabon shugaban Hukumar bayar da agajin gaggawa na kasa (NEMA).

Nadin da aka yi wa Muhammed zai fara aiki ne daga ranar Alhamis 30, ga watan Afrilun 2020 inda zai karbi ragamar mulkin hukumar daga tsohon shugaban ta Injiniya Mustaha Y. Maihaja.

A cewar sanarwar da Direktan watsa labarai na Ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Mista Wille Bassey ya fitar a yammacin ranar Asabar, Muhammad zai yi aiki na wa’adin farko na tsawon shekaru hudu.

Sanawar ta ce, “Nadin za ta fara aiki daga ranar Alhamis 30, ga watan Afrilun 2020 na waadin farko na shekaru hudu kamar yadda sashi na 3 na Dokar National Emergency Management Agency Act ta tanada.

“An umurci tsohon shugaban hukumar mai barin gado, Injiniya Mustaha Y. Maihaja ya mika dukkan takardu da bayyanai na ayyuka ga AVM Muhammadu Alhaji Muhammed (Mai ritaya) nan take.

“Shugaban kasar kuma ya mika godiyarsa da shugaban hukumar mai barin gado kana ya bukaci sabon shugaban ya yi aiki tukuru

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here