Isah Ahmed Daga Jos
COCIN Assemblies of God ta gundumar Saminaka da ke Jihar Kaduna, ta shirya taron wayar da kan mabiya cocin, kan matakan kariya kan cutar annobar Korona, tare da tallafa wa mabiya cocin mutum 80 da kayayyakin abinci a ranar juma’ar nan, a garin Saminaka
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban cocin na Assemblies of God na gundumar Saminaka, kuma wakilin shugaban cocin na kasa, a yankin jihohin Arewa ta yamma Rebaran Haruna Tutu, ya bayyana cewa sun shirya taro ne, domin su wayar da kan jama’a kan matakan da suka kamata su dauka, kan kare yaduwar cutar annobar Korona, da ta addabi duniya baki daya.
Ya ce sun debo wakilan wannan coci, na wannan gudunmawa ne daga wurare daban-daban, domin su je su isar da wannan sako, zuwa ga sauran mabiya cocin na gundumar baki daya.
Har ila yau ya ce sun fahimci cewa akwai bukatar su taimaka wa jama’a da kayayyakin abinci, saboda halin da ake ciki sakamakon dokar hana fita, da aka sanya.
Ya ce don haka suka tallafa wa mabukata na cocin, mutum 80 da kayayyakin abinci da suka hada da shinkafa da masara da taliya da ‘yan kudaden shiga mota domin komawa garuruwansu.
Ya ce sun bayar da wannan tallafi ne, domin su nuna goyon bayansu ga gwamnati, wajen tallafa jama’a ganin gwamnatin ba za ta iya tallafa wa kowa da kowa ba.
Ya yi kira ga al’umma su rika yin aiki da dokokin da aka shimfida, kan kare yaduwar wannan cuta.
A nasa jawabin shugaban babbar makarantar nazarin addinin kirista, ta T S N N da ke garin Saminaka, Dokta Benedict Kekung ya bayyana cewa dukkan matakan da gwamnati take dauka, kan kare yaduwar wannan cuta, tana yi ne domin ceto al’ummar Najeriya daga fada wa wannan mummunar annoba.
Don haka ya yi kira ga al’ummar Najeriya, su rika wanke hannayensu da sanya takunkumi a bakunansu guje wa cukuduwar jama’a, don kaucewa kamuwa da wannan annoba.