Gwamnatin Filato Ta Sassauta Dokar Hana Fita Zuwa Ranar Litinin

0
301

 Isah Ahmed Daga Jos

GWAMNATIN Jihar Filato ta dada sassauta dokar hana fita, da ta sanya zuwa daren ranar Litinin maimakon daren ranar Lahadi, kamar yadda ta sanar tun da farko. Wata sanarwa da ke dauke da sanya hanun Daraktan watsa labaran Gwamnan jihar, Dokta Makut Simon Macham ce ta bayyana haka.

Sanarwar ta ce gwamnatin ta dada sassauta  dokar ne sakamakon koke koken da jama’ar Jihar suka yi cewa ranar Juma’ar nan ta zo a ranar hutun ma’aikata ne. Don haka jama’a basu sami damar fitar da kudade daga bankuna da  sayen kayayyakin abinci ba.

Sanarwar ta ce don haka gwamnatin ta dada sassauta dokar, don ta baiwa jama’a dama suje su cire kudade a bankuna kuma su sayi kayayyakin abinci kafin daren ranar Litinin da dokar za ta ci gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here