Korona Bairos: Ma’aikatan Abuja Da Ke Jihohi Kada Su Dawo Aiki – FCTA

0
318

Rahoton Z A Sada

DUK da sassauta dokokin kulle da Shugaba Buhari na Najeriya ya yi daga ranar Litinin mai zuwa, hukumar babban birnin kasar, Abuja (FCTA) ta umarci ma’aikatan da ke zaune a wajen birnin da kada su koma.

Wannan umarni yana kunshe ne a wata sanarwa da Ministan Abuja Mallam Muhammad Bello ya fitar ranar Asabar, inda ya ce za a aiwatar da matakin sassauta dokar ne sannu-sannu.

“Kazalika, ma’aikatan da ke zaune a wajen birnin Abuja su ci gaba da zama a garuruwan da suke har sai an dage dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi,” in ji wani bangare na sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa dukkanin taruka haramun ne a birnin da suka hada da na biki da addini.

Har wa yau, wuraren taruwar jama’a kamar gidajen kallo da sinima da wasanni da shakatawa da na shan barasa, baki daya za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Game da sufuri kuwa, an haramta yin acaba ko okada a fadin Abuja, sannan ‘yan tasi mutum uku kacal za su dauka bayan direba, yayin da ‘yan adaidaita sahu za su dauki mutum biyu ban da direba. Su ma motocin bas za su dauki kashi 50% ne kawai na abin da ya kamata motar ta dauka.

A jawabinsa na ranar Talata ga ‘yan Najeriya, Shugaba Buhari ya ce za a dage dokar hana fita da aka saka a Abuja da kuma jihohin Legas da Ogun daga ranar Litinin mai zuwa.

Sai dai mazauna garururwan za su fita ne kawai daga karfe 6:00 na safe zuwa 8:00 na dare.

Mutum 214 ne suka harbu da cutar korona a Abuja ya zuwa ranar Juma’a – 36 daga cikinsu sun warke, uku sun rasa rayukansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here