Ku Fidda Ranar Daidaituwar Al’amura A Cikin Shekarar Nan – Shugaban NCDC

0
378

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN cibiyar yaki da cututtuka ma su yaduwa ta kasa (NCDC) Chikwe Ihekweazu, ya ce al’amura ba za su dadaita a Najeriya da sauran kasashen duniya a cikin shekarar nan ba, sai dai, watakila zuwa shekara ta gaba.

Da yake gabatar da jawabi a wurin wani taro, Ihekweazu ya ce matsin da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu tamkar sadaukarwa ce domin gyara gobensu
Da aka tambaye shi a kan lokacin da al’amura za su koma daidai; a janye dokar nesanta, a daina saka takunkumi da sauran dokokin hana walwala da aka saka saboda annobar covid-19, sai ya ce; “watakila zuwa shekara ta gaba “.

“Na san mun shiga wani sabon yanayi da ba mu saba da shi ba, haka sauran kasashen duniya suke fama da irin wannan kalubale da tunanin yaushe al’amura za su koma daidai.

“Maganar gaskiya ita ce, haka za mu ci gaba da rayuwa da annobar covid-19 har zuwa cikin wata shekarar, idan ma mun yi sa’a kenan.

“Yanzu kamata ya yi mu fara tunanin yadda za mu yi rayuwa mai tsafta a cikin annobar covid-19, mu na fatan sauye – sauyen da aka zo da su za su taimaka wa mutane wajen kare kansu da dakile yaduwar annobar ,” a cewarsa.Ihekweazu ya ce burinsa shine ganin ‘yan Najeriya sun ci gaba da kula da tsaftar muhalli da jikinsu hatta bayan annobar covid-19.

“Tsafta ta na da matukar muhimmanci kuma za ta taimaka wajen dakile yaduwar cututtuka ma su yawa ,” a cewarsa.

Shugaban na NCDC ya ce akwai babban kalubale wajen hana taron jama’a, inda ya ce; “zan fi son ganin jama’a suna amfani da fasahar zamani wajen sadarwa. Za mu yi tunanin a kan hanyoyin takaita taron jama’a a kasuwanni, wuraren ibada da wurin taron biki .”

Ya zuwa yanzu akwai jimillar mutane 2170 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

Mutane 351 daga cikin adadin sun warke, yayin da annobar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 68 a fadin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here