Matasa Sun Yi Wa Jami’an Tsaro Ruwan Duwatsu A Kasuwar Kaduna

0
423

c

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

AN samu ruda ni a kasuwar Barci da ke Tudun Wada yayin da wasu fusatattun matasa suka jefi jami’an tsaro da suka zo kasuwa suna korar mutanen da ke sayar da kayayyakin da gwamnati ba ta halasta siyarwa ba sakamakon dokar kulle ta Covid-19.

Lamarin ya faru ne a kan layin Ibrahim Taiwo road inda masu sayar da gwanjo suka baza kayayyakin su.

An gano cewa motocin jamian tsaro biyu ne suka iso kasuwar misalin karfe 12 na rana suka fara umurtar masu sayar da gwanjon su kwashe kayayyakin su su koma gida.

Wani mai sayar da kayan gwanjo, “Wasu abokan aikinmu sun fara kwashe kayansu, sai wasu ‘yan daba suka fara ihun “karya ne “karya ne” su kuma jami’an tsaro suka fara kokarin kwace wayoyin da suke daukar su bidiyo da shi.

“Daga bisani, wasu yara suka fara jifar jami’an tsaron da duwatsu hakan ya tilasta musu barin kasuwar a cikin motocinsu.”

Wani mai sayar da kayan masarufi Bello Idris ya ce an shiga rudani yayin da matasan suka far jifan jami’an tsaron.

Ya ce, “An shiga rudani saboda wasu masu sayar da kaya da masu shaguna sun rufe shagunan su sun fara gudu lokacin da matasan ke jifan jami’an tsaron.”

An gano cewa jamian tsaron sun kama mutum daya a lokacin da ake hayaniyar.

Wani jami’in KASTELEA da ba ya son a fadi sunansa ya ce ana ta jifar jamian tsaron kusa da shataletalen Tudun wada da ke kusa da inda abin ya faru.

Ya ce, “Eh, matasa sun jefi jami’an tsaro da duwatsu kusa da kasuwa domin ina iya ganin duwatsu masa yawa a kasa.”

Rahotanni sun bayyana cewa tuni dai hankula sun kwanta amma wasu masu shaguna sun rufe shagunansu sun tafi gida.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, ASP Jalige ya ce zai bincika lamarin kafin ya yi jawabi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here