Sankarau Da Zazabin Cizon Sauro Ke Kashe Mutane Ba Korona Ba – Gwamnatin Kano

0
384

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN jihar Kano a ranar Juma’a ta ce binciken da aka fara gudanarwa a kan mace macen da aka samu a jihar ya nuna cewa mafi yawa cikin wadanda suka mutu zazabin cizon sauro ne da sankarau suka kashe su.

Mafi yawa daga cikin su suna da wasu cututtuka da suke fama da su kamar hawan jini, ciwon suga da wasu cututtukan a cewar wakilin gwamnatin jihar.

Mai magana da yawun gwamna Ganduje, Salihu Yakasai ya cewa galibin wadanda suka mutu ba su samu kulawan likitoci ba kafin suka mutu.

Gwamnatin jihar tare da hadin gwiwa da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, da Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta Afirka da ta Najeriya, NDCD, suna bincike don gano abinda ya yi sanadin mace macen da wasu ke dangantawa da COVID-19.

Mista Yakasai a ranar Juma’a ya shaida cewa majinyatan da ke fama da wasu cututtukan “sun mutu ne don ba su samu kulawa daga asibitocin gwamnati da masu zaman kansu ba a lokacin ana fargabar COVID-19.”

Ya kuma ce mafi yawancin asibitoci masu zaman kansu a jihar ba su aiki saboda annobar ta korona.

Akwai yiwuwar wannan ya shima yana daga cikin dalilan da yasa aka samu mace macen da yawa a jihar. Ya ce gwamnan jihar ya gana da masu asibitoci masu zaman kansu a kan batun.

Ya kuma bayyana cewa mambobi hudu na kwamitin kar ta kwana na yaki da COVID-19 a jihar sun kamu da coronavirus.

Amma ya nuna rashin jin dadinsa yadda wasu mutane ke izgili game da lamarin da ya ce hakan na iya kawo koma baya cikin yaki da cutar da ake yi a jihar.

Ya ce ma’aikatan lafiya suna bukatar yabo ne da goyon baya ba cin mutunci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here