An Bude Birnin Tarayya Abuja Da Legas Bayan Makonni 5 A Rufe

0
419

Rahoton Z A Sada

A ranar Litinin umurni sassauta dokar hana fita ke soma aiki a babban birnin tarayyar Najeriya wato Abuja da cibiyar kasuwancin kasar, wato Legas a wani mataki na takaita gurguncewar tattalin arzikin kasar wadda ita ce kasa mafi karfin tattallin arziki a fadin Nahiyar Afirka.

Wannan sabon umurni na nufin za a bude shaguna da kasuwanni daga safe har zuwa 3 na rana, Sai dai haramcin gudanar da taro zai ci gaba da aiki,kuma babu batun bude makarantu da wuraren ibada.

Wasu ma’aikata za su koma bakin aikinsu, sannan dokar hana zirga-zirga za ta yi aiki da daddare.

Har wa yau, an sanya wajabci kan sanya takunkumi da kuma zama nesa-nesa da juna domin hana yaduwar cutar.

Najeriya dai na ci gaba da samun karuwar alkalumma mutane da ke kamuwa da cutar korona inda sabbin alkaluman hukumar dakile cutuka ta kasar ke cewa sama da mutum dubu biyu da dari biyar ne suka kamu da cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here