Kasashen Gabas Ta Tsakiya Da Kasashen Turai Na Sassauta Dokar Kulle

0
283

Rahoton Z A Sada

KASAR Tunisiya ta sassauta dokar kulle da ta kakaba na tsawon mako shida. Kusan rabin ma’aikatan gwamnati da kamfanoni za su koma bakin aikinsu, sannan amfani da takunkumi wato face mask zai zama wajibi.

Masar za ta bai wa otel-otel damar budewa ga baki ‘yan yawon bude ido tsakanin jihohin kasar, kan sharudan rage adadin mutane da suke karba da kashi 25 cikin 100.

Middle East

A Lebanon ma kantunan sayar da abinci da gyaran gashi za su bude, kuma mutane za su iya fita motsa jiki da shan iskar bakin teku.

A Iran za a bude masallatai a birane da dama da ba a samu yaduwar cutar da yawa ba.

Haka kuma kasahen Turai da dama na ci gaba da daukan matakan sassauta dokar kulle.

Turai

Daga cikinsu akwai Fotugal (Portugal) da Sifaniya (Spaniya) da Koroshiya (Croatia) da Girka, inda za a bude kananan shaguna da shagon gyaran gashi a yau Litinin.

Wasu makarantu za su bude a yau a Jamus da Austria, yayin da a Hungary da Serbia da Slovenia kantunan cin abinci da barasa za su soma aiki bisa sharudan wasu matakai.

Poland kuma za ta bai wa Otel-Otel da manyan shagunan da wasu gidajen adana kayan tarihi damar sake budewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here