Korona Bairos: Gwamna Tambuwal Ya Sanya Dokar Hana Zirga-zirga A Sakkwato

0
373

Rahoton Z A Sada

GWAMNAN jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya ce jihar na fuskantar karuwar masu dauke da cutar korona inda ya zuwa ranar Lahadi adadin masu cutar a jihar ya kai 66 sannan kuma mutum 8 sun mutu.

Saboda haka ne Gwamnan ya ce daga ranar Litinin din nan gwamnati ta sanya dokar hana zirga-zirga daga karfe 8:00 na dare zuwa karfe 6:00 na safe.

Wannan dai na dauke a cikin wani jawabi da ya yi wa ‘yan jihar a ranar Lahadi domin sanar da su irin halin da jihar ke ciki dangane da annobar korona.

Gwamna Tambuwal ya kuma nemi ‘yan jihar da su rungumi al’adar wanke hannaye da kuma yin nesa-nesa da juna

Daga karshe gwamna Tambuwal ya yi kira ga gwamnatin Tarayya da ta kai wa jihar ta Sakkwato dauki ta hanyar kayan aiki da manufar dakile yaduwar annobar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here