An Mayar Wa Najeriya Dala Miliyan 311 Cikin Kudin Abacha

0
288
An zargin marigayin da sace kimanin dala biliyan 2.2 daga babban bankin Najeriya

Rahoton Z A Sada

MINISTAN shari’a na Najeriya Abubakar Malami ya ce gwamnati ta karbi sama da dala miliyan 311 daga Amurka daga cikin kudaden da ake zargin tsohon shugaban mulkin soja Janar Sani Abacha ya sace.

A wata sanarwa da maitaimaka masa kan yada labarai Dakta Umar Jibril Gwandu ya fitar ranar Litinin, ya ce kudin ruwa ya sa kudaden sun karu daga dala miliyan 308 zuwa dala miliyan 311 daga watan Fabrairun 2020 da aka ajiye su a Babban Bankin Najeriya zuwa 28 ga Afrilu.

Sanarwar ta ce tun 2014 gwamnatin Najeriya ta fara bin matakai na dawo da kudaden da ake kira “Abacha III.”

Malami ya shaida wa BBC cewa an dawo wa Najeriya da kudaden ne bayan jayayya da kuma samun daidaituwa da fahimtar juna tsakanin gwamnatin Amurka da gwamnatin Jersey da aka boye kudaden na Abacha.

Amma ya ce Amurka da Jersey sun karbi wani kaso na kudin saboda kai kawon shari’a da kokarin kwatar kudaden.

Malami ya ce za a yi amfani da kudaden wajen kammala ayyuka a sassan Najeriya da suka hada da hanyar Legas zuwa Ibadan da hanyar Abuja zuwa Kano da kuma gadar Niger.

Ana dai zargin marigayi Sani Abacha da sace kimanin dala biliyan 5 a lokacin mulkinsa daga shekarar 1993 zuwa 1998 lokacin da ya rasu.

Tun a shekarar 1999, aka soma batun kudaden da ake zargin Janar Abacha ya sace kuma hukumomi a Switzerland sun dawo wa gwamnatin Najeriya da wasu daga cikin kudaden.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here