Ma’aikatan Lafiya 14 Sun Kamu Da Cutar Korona A Katsina

0
422

Rahoton Z A Sada

AKALLA ma’akatan lafiya 14 ne suka kamu da cutar korona a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.

Jaridar ThisDay, wacce ta ambato Gwamnan jihar Aminu Bello Masari yana tabbatar da hakan a hirar da ya yi da manema labarai ranar Litinin, ta kara da cewa ma’aikatan sun harbu da cutar ne lokacin kula da masu dauke da korona.

Ya kara da cewa 10 daga cikinsu ma’akatan Federal Medical Centre, Katsina ne, yayin da hudu kuma ma’aikatan asibitoci masu zaman kansu ne.

Gwamna Masari ya ce an samu karin mutum 37 da suka kamu da cutar korona a jihar, inda jimilla ake da mutum 75 da suka harbu da cutar a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here