Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Ya Mutu A Kano

0
480

Daga Usman Nasidi.

RAHOTANNI daga jihar Kano na bayyana cewa Allah Ya yi wa Mataimakin Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Atiku Nagodi rasuwa a ranar Litinin da ta gabata.

Mataimakin Kwamishinan ‘yan sandan Nagodi, ya mutu ne bayan wata gajeriyar jinya.

Mutuwar Nagodi na daga cikin adadin mutanen da ke ci gaba da mutuwa a jihar Kano.

Sai dai, ya zuwa yanzu babu wasu isassun bayanai dangane da mutuwar babban jami’in dan sandan, haKazalika, rundunar ‘yan sanda ba ta fitar da jawabi ba.

Nasir Gwarzo, jagoran tawagar ma’aikatan lafiya da aka tura Kano, ya ce su na zargin cewa annobar cutar covid-19 ce sanadiyyar mutuwar mutane a jihar.

Dakta Nasiru Sani Gwarzo ya bayyana cewa cutar COVID-19 ce ta ke kashe mutane a ‘yan kwanakin nan a jihar Kano.

Nasiru Sani Gwarzo ya ce binciken da su ka yi ne ya nuna masu haka.

Kwararren likitan wanda ya na cikin masu yaki da annobar Coronavirus ya shaidawa manema labarai cewa sakamakon gwajin da su ka yi ya nuna COVID-19 ce ke kashe jama’a.

Gwarzo ya yi wannan jawabi a ranar Lahadi, 3 ga watan Mayu, 2020, ya ce sakamakon binciken
mace – macen da ake yi a ‘yan kwanakin baya bayan nan, ya tabbatar cewa akwai hannun cutar.

Dakta Nasiru Gwarzo ya fadi hakan ne yayin da ya ke magana da ‘yan jarida bayan bikin kaddamar da wani dakin gwaji da Alhaji Aliko Dangote ya gina a Kano.

A cewar Dakta Nasiru Gwarzo: “ Bari in sanar da ku cewa a mafi yawan mace-macen da aka yi kwanan nan, daga gwajin da aka yi, an gano cewa cutar Coronavirus ce sanadin mutuwar .”

Ya ce: “ Saboda kafin cikakken rahotonmu ya fito nan da mako guda ko kuma ‘yan kwanaki, ya zama dole mutanen jihar Kano su farka daga gyangyadin da su ke yi game da annobar.”

“Ba sabon abu ba ne, kasashen Duniya irinsu Amurka, Sin, Italiya, Sifen, Ingila da Faransa da sauransu, sun yi fama da irin wannan mace-mace mai ban mamaki .” Inji Dakta Gwarzo.

Kwanakin baya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya turo Nasiru Sani Gwarzo da tawagarsa su zo jihar Kano domin su binciki abin da ya ke jawo mutuwar Bayin Allah bini-bini.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here