‘Yan Kasuwa A Kaduna Suna Kwashe Kayansu

0
278
Mustapha Imrana Abdullahi
SAKAMAKON irin yadda duniya ke fama da batun Covid -19 da ake kira da korona, lamarin da ya sa gwamnatin jihar Kaduna ta kulle kasuwanni da suka hada da babbar kasuwar Kaduna wato kasuwar Sheikh Abubakar Gumi da ke cikin garin Kaduna.
Kamar yadda wakilinmu ya zagaya cikin garin Kaduna ya tarar dimbin ‘yan kasuwar da suka hada da maza da mata suna ta kokarin kwashe kayansu daga kasuwar, kasancewar sun shafe kwanaki sama da 30 kasuwar na rufe.
Kamar yadda wakilinmu ya ji ta bakin wani dan kabilar Igbo da ke da rumfar sayar da Takalmi a cikin kasuwar dan kasuwar ya koka da cewa su har yanzu ba su san inda za su koma ba domin gudanar da kasuwancinsu ta yadda za su samu abin sakawa cikin bakinsa.
Wakilin namu ya kuma ji ta bakin wasu yan kasuwar inda suka shaida masa cewa gara su kwashe kayansu domin barinsu a cikin kasuwar ba zai kara masu komai ba.
Sai kuma wadansu da ke da tunanin su rika zuwa Makarantun Firamaren da gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa a rika kai kayan abinci da magunguna ana sayarwa wato kasuwannin Unguwanni.
Wakilinmu yaga irin yadda wasu daga cikin yan kasuwar ke zuba kayansu a cikin motocinsu suna wucewa zuwa gidajensu domin samun mafita daga baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here