Za A Kai Wadanda Suka Yi Rufa-rufa Kotu A Kaduna – Kwamishina

0
398

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNATIN jihar Kaduna ta yi gargadi cewa duk wanda aka samu ya na boye wani abu game da lafiyarsa ko a kan masu dauke da cutar COVID-19 zai gamu da fushin hukuma a gaban kotu.

Kwamishinar yada labarai ta jihar Kaduna, Dakta Amina Mohammed-Baloni ta shaida wa ‘yan jarida wannan, tare da bayyana irin nasarorin da gwamnatin Kaduna ta cimma a wajen yaki da cutar.

Amina Mohammed-Baloni ta ce sun iya gano har 95% na wadanda su ka samu alaka da masu dauke da COVID-19 a jihar Kaduna. Kwamishinar ta ce sun gano mutane 28 da ke da cutar.

Dakta Baloni ta ce daya daga cikin wadanda su ka mutu a sanadiyyar cutar wani tsohon ma’aikacin gwamnati ne wanda ya boyewa likitoci cewa ya ziyarci jihar Kano a ‘yan kwanakin nan.

“A sakamakon haka aka kwantar da shi a dakin killace marasa lafiya da sunan ya na fama da cutar numfashi. A nan ya mutu kafin a fito da sakamakon gwajin COVID-19 da aka yi masa.”

Saboda masu yin irin wannan karya, kwamishinar lafiyar ta ce gwamnatin Kaduna za ta rika gurfanar da duk wanda aka samu ya yi wa ma’aikatan asibiti karya game da halin lafiyarsa.

Wannan Bawan Allah ya kai ziyara zuwa Kano a cikin kwanakin nan. Amma da aka je asibiti, sai ya nuna cewa sam ba haka ba. A karshe cutar ta kashe shi kafin malaman asibitin su farga.

Jihar Kano mai makwabtaka da Kaduna ta na cikin inda cutar ta yi kamari a halin yanzu a Najeriya. Mafi yawan almajiran da ke dauke da COVID-19 a Kaduna sun dawo ne daga Kano.

Kawo yanzu Dakta Amina Baloni ba ta bayyana laifin da za a kama wadanda su ka boye gaskiyar lamarin lafiyarsu ba. Gwamnatin Kaduna ta na ta kokarin ganin bayan wannan annoba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here