An Kwantar Da Sarkin Daura A Asibitin Tarayyar Jihar Katsina

0
583

Daga Usman Nasidi.

AN kwantar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar a sashen kula ta musamman ta asibitin tarayya da ke jihar Katsina.

Wata majiya daga fada a ranar Talata ta ce an gaggauta mika Umar asibiti a daren Litinin kuma an kwantar da shi sakamakon mawuyacin halin da yake ciki.

Ana zargin Umar ya kwashi cutar COVID-19 daga likitan jihar Katsina, Dakta Aminu Yakubu, wanda ya rasu sakamakon cutar a watan da ya gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayi Yakubu ne likitan mai martaba sarkin Daura Umar Farouk da matarshi, Hajiya Binta Umar kafin mutuwarsa.

Matar sarkin Daura, Hajiya Binta Umar Farouk ta rasu a makonni biyu da suka gabata.

“A daren jiya ne aka hanzarta miki sarkin Daura asibitin tarayya da ke Katsina. A halin yanzu, an umarcemu da mu killace kanmu.

“Likitan da cutar ta kashe a jihar ya yi mu’amala da sarkin Daura da matarsa wacce ta rasu. Likitan ne ke duba lafiyar basaraken da matarsa.

“An umarci sarkin da ya killace kansa tun bayan mutuwar likitan amma bai saurara hakan ba. Ya bari ana shige da fice a fadar.”

A ranar Litinin ne Dakta Mustapha Inuwa, sakataren gwamnatin jihar Katsina yace an samu wasu
masu dauke da cutar a fadar.

An diba samfur din mutum 89 amma har yanzu suna hannun NCDC don gwaji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here